=Kalmomin Rai","Bishara","Waƙoƙin Bishara"-Harsunan da ake Magana a Nigeria Inda Kiristoci 'yan tsiraru ne (Lamba 200-223) //" "Words of Life","Good News","Gospel Songs"-in Nigeria, These People Have Ethnic or Islam as their Major Religion(No.200-223)=

Federal Republic of Nigeria Words of Life 8

====="Kalmomin Rai","Bishara","Waƙoƙin Bishara"-Harsunan da ake Magana a Nigeria Inda Kiristoci 'yan tsiraru ne (Lamba 200-223) ===== (Hausa, English, English African, Tai, Tala, Tembis(Rom), Tapshin:Tapshinawa(Kusur-Myet), Teme(Tema), Tiba (Gaa), Tigon (Mbembe), Tsagu(Ciwogai), Tuareg:Tamajaq(Tawallammat), Tubu:Teda(Tedaga), Turkwam(Atoro), Ukaan, Uneme, Ungwai(Ca̱hungwa̱rya̱), Ura(Fungwa), Vemgo:Mabas(Visik), Verre, Wagga(Waja), Warji(Warjawa), Wom[Nigeria], Yala, Yachi(Hasha), Yotti, Ywom, Zarma(Zarmaciine), Zeem) ===== "Words of Life","Good News","Gospel Songs"-in Nigeria, These People Have Ethnic or Islam as their Major Religion(No.200-223) ===== read less
Religion & SpiritualityReligion & Spirituality

Episodes

Turanci Ruhaniya Song - "Akwai Buri A Cikin Zukatanmu".3gp
Jan 1 2023
Turanci Ruhaniya Song - "Akwai Buri A Cikin Zukatanmu".3gp
English Spiritual Song - "There Is a Longing in Our Hearts".3gp // John - Chapter 11 In the beginning was the Word: the Word was with God and the Word was God.2 He was with God in the beginning.3 Through him all things came into being, not one thing came into being except through him.4 What has come into being in him was life, life that was the light of men;5 and light shines in darkness, and darkness could not overpower it.6 A man came, sent by God. His name was John.7 He came as a witness, to bear witness to the light, so that everyone might believe through him.8 He was not the light, he was to bear witness to the light.9 The Word was the real light that gives light to everyone; he was coming into the world.10 He was in the world that had come into being through him, and the world did not recognise him.11 He came to his own and his own people did not accept him.12 But to those who did accept him he gave power to become children of God, to those who believed in his name 13 who were born not from human stock or human desire or human will but from God himself.14 The Word became flesh, he lived among us, and we saw his glory, the glory that he has from the Father as only Son of the Father, full of grace and truth.15 John witnesses to him. He proclaims: 'This is the one of whom I said: He who comes after me has passed ahead of me because he existed before me.'16 Indeed, from his fullness we have, all of us, received -- one gift replacing another,17 for the Law was given through Moses, grace and truth have come through Jesus Christ.18 No one has ever seen God; it is the only Son, who is close to the Father's heart, who has made him known.
Harshen  Hausa - "The Hanyoyi Biyu".mp3
Jan 1 2023
Harshen Hausa - "The Hanyoyi Biyu".mp3
Hausa Language - "The Two Roads".mp3 // YAH 1. - Kalman Ya Zama Mutum1Tun fil'azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake, Kalman nan kuwa Allah ne.  2Shi ne tun fil'azal yake tare da Allah.  3Dukan abubuwa sun kasance ta gare shi ne, ba kuma abin da ya kasance na abubuwan da suka kasance, sai ta game da shi.  4Shi ne tushen rai, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane.  5Haske na haskakawa cikin duhu, duhun kuwa bai rinjaye shi ba.6 Mat 3.1; Mar 1.4; Luk 3.1,2 Akwai wani mutum da Allah ya aiko, mai suna Yahaya.  7Shi fa ya zo shaida ne, domin ya shaidi hasken, kowa yă ba da gaskiya ta hanyarsa.  8Ba shi ne hasken ba, ya zo ne domin ya shaidi hasken.9Akwai hakikanin haske mai shigowa duniya da yake haskaka kowane mutum.  10Dā yana duniya, duniyar ta wurinsa ta kasance, duk da haka duniya ba ta san shi ba.  11Ya zo ga abin mulkinsa ne, jama'a tasa kuwa ba ta karɓe shi ba.  12Amma duk iyakar waɗanda suka karɓe shi, wato, masu gaskatawa da sunansa, ya ba su ikon zama 'ya'yan Allah,  13wato, waɗanda aka haifa ba daga jini ba, ba daga nufin jiki ko nufin mutum ba, amma daga wurin Allah.14Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa.15Yahaya ya shaida shi, ya ɗaga murya ya ce, “Wannan shi ne wanda na ce, ‘Mai zuwa bayana ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.’ ”  16Dukanmu kuwa daga falala tasa muka samu, alheri kan alheri.  17Domin Shari'a, ta hannun Musa aka ba da ita, alheri da gaskiya kuwa ta wurin Yesu Almasihu suka kasance.  18Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai. Makaɗaicin Ɗa, wanda yake yadda Allah yake, wanda kuma yake a wurin Uba, shi ne ya bayyana shi.
Hausa(حَوْسَ) -"Yesu: Ubangiji kuma Mai Ceto".3gp
Jan 1 2023
Hausa(حَوْسَ) -"Yesu: Ubangiji kuma Mai Ceto".3gp
Hausa(حَوْسَ) -"Jesus: Lord and Saviour".3gp // 1KOR 13. - Ƙauna1Ko da zan yi magana da harsunan mutane, har da na mala'iku, amma ya zamana ba ni da ƙauna, na zama ƙararrawa mai yawan ƙara ke nan, ko kuwa kuge mai amo.  2Mat 17.20; 21.21; Mar 11.23 Ko da zan yi annabci, ina kuma fahimtar dukkan asiri, da dukkan ilimi, ko da kuma ina da matuƙar bangaskiya, har yadda zan iya kawar da duwatsu, muddin ba ni da ƙauna, to, ni ba kome ba ne.  3Ko da zan sadaukar da duk abin da na mallaka, in kuma ba da jikina a ƙone, in har ba ni da ƙauna, to, ban amfana da kome ba.4Ƙauna tana sa haƙuri da kirki. Ƙauna ba ta sa kishi, ba ta yin kumbura.  5Ƙauna ba ta sa ɗaga kai ko rashin kārā, ƙauna ba ta sa sonkai, ba ta jin tsokana, ba ta riƙo.  6Ƙauna ba ta sa yin farin ciki da mugunta, sai dai da gaskiya.  7Ƙauna tana sa daurewa a cikin kowane hali, da bangaskiya a cikin kowane hali, haka kuma sa zuciya a cikin kowane hali, da jimiri a cikin kowane hali.8Ƙauna ba ta ƙarewa har abada. Annabci zai shuɗe, harsuna za su ɓace, ilimi kuma zai shafe.  9Ai, hakika iliminmu ba cikakke ba ne, annabcinmu kuma ba cikakke ba ne.  10Sa'ad da kuwa cikakken ya zo, sai ɗan kiman nan yă shuɗe.  11Sa'ad da nake yaro, nakan yi magana irin ta ƙuruciya, nakan yi tunani irin na ƙuruciya, nakan ba da hujjojina irin na ƙuruciya. Da na isa mutum kuwa, sai na bar halin ƙuruciya.  12Gama yanzu kamar a madubi muke gani duhu duhu, a ranar nan kuwa za mu gani ido da ido. A yanzu sanina sama sama ne, a ranar nan kuwa zan fahimta sosai, kamar yadda aka fahimce ni sosai.  13To, a yanzu abubuwan nan uku sun tabbata, bangaskiya, da bege, da kuma ƙauna, amma duk mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna.