Kayan Mata: Gyaran Jiki Ko Janyo Ciwo?

Daga Laraba

Aug 17 2022 • 30 mins

Maganin mata da aka fi sani da kayan mata ya samu karbuwa a tsakanin mata musamman na Arewacin Najeriya.

Amma wai da gaske ne waɗannan hade-haden da mata ke sha wani lokacin kuma su yi kunzugu dashi na amfanin da ake saya domin sa?

Shirin Daga Laraba ya bigi jaki ya bigi taiki, domin kuwa ya tattauna da masu hada irin wadannan magunguna da masu saya, da ma wadanda ake saya domin su da kuma likitoci domin fayyace gaskiyar amfani da illar kayan mata.

Domin sauke shirin kai tsaye latsa nan