Dalilin Da 'Yan Boko Haram Ke Yanka 'Yan Jari Bola A Maiduguri

Najeriya a Yau

Jun 21 2022 • 14 mins


A 'yan kwanakin nan rahotanni sun bayyana cewa 'yan boko haram sun yanka 'yan jari bola sama da 50 a kasa da kwana 30 a Jihar Borno.

Irin wannan hari dai ba kasafai ake samun irinsa ba. Ko me ya janwo hakan?

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattauna da masu ruwa da tsaki daga Jihar Borno kan yadda abin ya kasance, wadanda aka kashe da kuma dalilin makasan.