Ayyuka Na Musamman A Kwanaki 10 Farkon Watan Dhul-hijja

Najeriya a Yau

Jul 1 2022 • 15 mins


Watan Dhul-hijja ne wata na 12 a jerin watannin kidaya a addinin Musulunci. A cikin wannna wata ake aikin hajji, babbar sallah da layya.

Akwai ayyuka na musamman da malamai suka bayyana a matsayin ayyukan da Allah ke so kuma suke sa Shi ya jikan bayinsa ya gafarta musu.

Mun tattaro irin ayyukan da ya kamata Musulmi ya gudanar a cikin wadannan kwanaki masu daraja.