‘Yadda Aka Nemi Yin Lalata Da Ni A Wurin Aiki’

Najeriya a Yau

Jul 5 2022 • 15 mins


Shin me ke sa a wasu wuraren aiki ake neman yin lalata da ma’aikata?

Duk da cewa an fi neman mata domin yin lalata da su a wuraren aiki, bincike ya nuna yanzu lamarin ya kai ga har mazan ma ba a bari ba.

Shirin Najeriya A Yau ya tattauna da wata wadda ta taba samun kanta a irin wannan yanayi, ta kuma ji ta bakin da masana da sauran masu sharhi a kan wannan matsala.