Tasirin Kawancen NNPP Da ‘Labour Party’ A Zaben 2023

Najeriya a Yau

Jun 30 2022 • 13 mins


Yunkurin neman jam’iyyar da za ta hana jam’iyyar APC zarcewa a mulki da kuma hana PDP dawowa kan mulki a Najeriya ya sa hankalin manazarta siyasa kallon rade-radin kawance tsakanin Jam’iyyar NNPP da Labour Party a matsayin mafita ga masu irin wancan tunani.

Amma shin da gaske ne akwai maganar kawancen?

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya binciko irin tasirin da wannan kawance zai yi idar har ta tabbata.