Yadda Muke So A Tsayar Da ’Yan Takara A Zaben 2023 —CAN

Najeriya a Yau

Jun 14 2022 • 14 mins


Tun bayan kammala zaben dan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya aka fara tunanin wanda zai yi wa dan takarar jam'iyyar Bola Ahmed Tinubu mataimaki.

Kungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) ta gargadi jam’iyyar da cewa kar su sake su bari a yi shugaba Musulmi mataimaki ma Musulmi.

Wannan kira na CAN ya janyo martani daga wurin jama'ar kasar.Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tuntubi kungiyar ta kuma ji matsayar kungiyar Musulmi ta JIBWIS kan wannan batu.